Yanzu Yanzu: Babban hadimin Dogara ya bar APC

Yanzu Yanzu: Babban hadimin Dogara ya bar APC

Usman Bawa, babban mai ba kakakin majalisar wakilai shawara kan ayyuka na musamman a ranarr Litinin, 16 ga watan Yuli ya rubuta takardan barin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Mista Bawa ya kasance dan majaliar wakilai inda yake wakiltan karamar hukumar Kaduna ta arewa a majalisar dokokin kasar.

Ya aika wasikar dauke da sa hanunsa zuwa ga shugaban APC a karamar hukumarsa.

Yanzu Yanzu: Babban hadimin Dogara ya bar APC

Yanzu Yanzu: Babban hadimin Dogara ya bar APC

A shekarar 2015 kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya nada Bawa.

KU KARANTA KUMA: Bana tsoron EFCC, ba zan gudu na bar Najeriya ba - Fayose

Kakakin Dogara, Turaki Hassan ya tabbatar da cewa har yanzu Bawa na a matayinsa na hadimin maigidansa.

Bai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai koa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel