Ku daina ganin laifin Buhari akan kashe-kashe – MURIC ga yan Najeriya

Ku daina ganin laifin Buhari akan kashe-kashe – MURIC ga yan Najeriya

Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta shawarci yan Najeriya da su daina ganin laifin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kashe-kashen da ake yi a fadin kasar.

Kungiyar ta bayar da wannan shawara ne a wata sanarwa da daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ya saki ga manema labarai a ranar Litinin a garin Ibadan.

Akintola ya laifin yan siyasa, kabilaci da kafafen watsa labarai wajen yada bayanan karya game da kashe-kashen da ake yi a kasar.

Ku daina ganin laifin Buhari akan kashe-kashe – MURIC ga yan Najeriya

Ku daina ganin laifin Buhari akan kashe-kashe – MURIC ga yan Najeriya

Yace ba ayi adalci ba idan aka ga laifin Buhari kan rashin dakatar da kashe-kashe saboda tsaro hakki ne da ya rataya a wuyan mutane da dama musamman a matakan gwamnati daban-daban.

KU KARANTA KUMA: Bana tsoron EFCC, ba zan gudu na bar Najeriya ba - Fayose

Akintola yace bayanin da Hon. Ahmed Maje yayi kwanan nan cewa wasu yan siyasa ke daukar nauyin masu kashe-kashe da kuma wadanda ake horarwa a kasar Isra’ila ya rigada ya nisanta Buhari daga kashe-kashen.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel