Karanta irin abinda Obama yayi da kakarsa lokacin da yaje kauyen su

Karanta irin abinda Obama yayi da kakarsa lokacin da yaje kauyen su

- Gidan talabijin din Kenya sun nuna tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama yana taka rawa da kakarsa.

- Obama dai shine bakar fata na farko daya mulki kasar Amurka.

Karanta irin abinda Obama yayi da kakarsa lokacin da yaje kauyen su

Karanta irin abinda Obama yayi da kakarsa lokacin da yaje kauyen su

Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama yakai ziyara kauyen su dake kasar Kenya a ranar Litinin dinnan, inda ya taka rawa irinta gargajiya shi da kakarsa, wannan dai itace ziyara ta farko da yakaiwa kauyen tun bayan barinsa mulki.

Yaje kasar ta Kenya ne a dalilin kaddamar da wata cibiyar matasa da yar uwarshi Auma Obama ta kafa.

DUBA WANNAN: NBC ta ceto jihar Ekiti daga mummunan rikici - Falana

Kafafen yada labarai na kasar Kenya sun nuna tsohon Shugaban kasar na Amurka tare da kakarsa Sarah Obama a yayin da suke taka rawar gargajiya.

Bayan isar Obama kasar a ranar Lahadi ya gana da Shugaban kasar ta Kenya, Uhuru Kenyatta wanda ya saka a shafinsa na Twitter "muna farin ciki da dawowar ka @BarackObama."

Daga kasar ta Kenya Obama zai wuce kasar Afrika ta Kudu a ranar Talata inda zai bada jawabi akan shekaru 100 na Nelson Mandela. Jawabin da zai gabatar a ranar shine dai zai zamo jawabin sa na farko da zai gabatar a cikin taron mutane tun bayan barinsa mulki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel