NBC ta ceto jihar Ekiti daga mummunan rikici - Falana

NBC ta ceto jihar Ekiti daga mummunan rikici - Falana

- Mr Femi Falana yace ba karamin kokari kafar yada labarai ta kasa tayi ba data rufe kafafen yada labarai na jihar Ekiti.

- NBC ta cancanci yabo ta hanyar rufe dukkanin gidan talabijin da radio dake jihar ta Ekiti.

NBC ta ceto jihar Ekiti daga mummunan rikici - Falana

NBC ta ceto jihar Ekiti daga mummunan rikici - Falana

Lauyan dake kare hakkin dan adam Mr. Femi Falana yace rufe kafofin yada labarai da hukumar yada labarai tayi dake jihar Ekiti shine kadai zai hana afkuwar rigingimu a jihar lokacin da zaben daya gabata.

Gwamnan jihar Mr Ayo Fayose ya fito kafar yada labarai inda ya bayyana sakamakon zabe da aka gudanar inda yace jam'iyar PDP wacce mataimakin sa Prof Kolapo Olusola ya fito itace ta lashe zaben, inda NBC tace hakan ya sabawa tsarin kafofin watsa labarai.

DUBA WANNAN: APC ta bukaci Saraki ya bayyanawa al'umma jam'iyyar da yake

Falana yayi kira ga sabon gwamnan jahar Ekiti Dr Kayode Fayemi da yayi amfani da wannan damar idan ya karbi ofishin wajen kawo karshen ta'addanci da jihar ke fama dashi.

Yace "NBC ta cancanci yabo ta hanyar dakatar da gidajen Talabijin da radio data yi saboda sanar da sakamakon karya da gwanma Ayo Fayose yayi.

"Sannan ina kira ga hukumar zabe ta kasa (INEC) data kawo karshen karin kuri'u da akeyi a zaben gwamna na jihar Osun da zai gudana anan gaba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel