Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Benue ya fita daga APC

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Benue ya fita daga APC

Kamar yadda akayi hasashe, gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana a yau Litinin, 16 ga watan Yuli cewa ya bar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a gidan gwamnatin jihar da ke garin Makurdi.

Ortom yayinda yake rantsar da sabon mai bashi sgawara na kananan hukumomi, Jerome Torshimbe, ya bayyana cewa an koreshi daga jam’iyyar APC

Yace: “ Game da jam’iyya kuwa, an koreni daga jam’iyyar. Ina waje yanzu. Kuma idan aka baiwa mutum jan kati, wannan na nufin cewa yanada na cewa na kansa.”

Wannan abu da gwamnan jihar Benue ya bayyana yayi dai-dai da has ashen da akeyi tun kwanakin baya cewa gwamnan na cikin gwamnonin Arewa uku da ke shirin barin jam’iyyar kuma tuni jam’iyyar na shirin maye gurbinsa da wani a zaben 2019.

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Benue ya fita daga APC

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Benue ya fita daga APC

KU KARANTA: Kwamitin mutum 11 zai soma bincikar Obasanjo da Jonathan kan badakalar satar kudi

Gwamnan dai har yanzu bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba amma idan ya yannke shawara, zai bayyanawa mutanen jihar Benue.

Ya kara da cewa: “Ban san abinda zai faru ba amma ina jira. Idan wasu suka zo, zan bayyanawa mutan jihar Benue kungiyar da zan koma.”

Ya yi kira ga mutanen jihar da su kasance tsintsiya madaurinki daya kuma kada su bari banbamcin jam’iyya ko harshe ya raba kansu. Yace Ubangijin da ya bashi nasara a 2015 ne zai taimaka masa a zabe mai zuwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel