Wasu dalibai sun shiga tasku bayan mallakar bindigu a jihar Filato

Wasu dalibai sun shiga tasku bayan mallakar bindigu a jihar Filato

- Idon wasu samari ya raina fata bayan gurfanar da su gaban kuliya

- An dai kama su ne da laifin mallakar bindigu ba bisa ka'ida ba

- Tuni dai kuliya ya tankada keyarsu gidan kaso don hakan ya zama izna ga 'yan baya

A yau Litinin ne wata babbar kotu dake zamanta a yankin kasuwan Nama a garin Jos ta yankewa wasu daliban kwalejin Panshin dake jihar Filato hukuncin daurin shekaru biyu a gidan kaso bisa laifin mallakar bindiga ba bisa ka'ida ba.

Wasu dalibai sun shiga tasku bayan mallakar bindigu a jihar Filato

Wasu dalibai sun shiga tasku bayan mallakar bindigu a jihar Filato

Alkalin kotun, Yahaya Mohammed ya yankewa daliban Panret Jacob mai shekaru 22 da kuma Peter Wunying mai shekaru 24 hukuncin zama a gidan kaso har tsawon watanni shida ba tare da tara ba, sai kuma hukuncin zama a gidan kaso na tsawon shekaru biyu ko kuma su biya tarar dubu 20,000 bisa laifin mallakar makami ba bisa ka'ida ba.

KU KARANTA: Kotu ta damkawa EFCC wata makekiyar kadara

Mai shari’a Mohammed yace wannan hukunci da aka yanke zai zama izina ga masu hali irin wannan wajen mallakar makamai masu hadari ba bisa ka'ida ba.

Kamfanin dillancin labarai ya rawaito cewa daliban sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da shi ba tare da kai ruwa rana ba.

Anthony Enegbenore wanda shi ne mai gabatar da shari'a a gaban kotu ya bayyana cewa an kama yaran ne da bindigogi kirar hannun har guda biyu, sai kuma akwatin harsashi wanda hakan ya saba da tanadin doka karkashin sashi na 27 na mallakar makami.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel