Bana tsoron EFCC, ba zan gudu na bar Najeriya ba - Fayose

Bana tsoron EFCC, ba zan gudu na bar Najeriya ba - Fayose

Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya bayyana cewa ba zai gudu ya bar Najeriya ba idan har kariya da yake da shi na bincikar laifinsa yak are a watan Oktoba 2018.

Kakakin Fayose, Lere Olayinka, ya bayyana a ranar Lahadi, 15 ga watan Yuli cewa yayi Magana da gwamnan kan makomarsa ba tare da kariya ba cikin sa’o’i 24 da suka shige.

Olayinka yace Gwamna Fayose ba zai bar kasar ba idan wa’adin mulkinsa ya cika, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Bana tsoron EFCC, ba zan gudu na bar Najeriya ba - Fayose

Bana tsoron EFCC, ba zan gudu na bar Najeriya ba - Fayose

Ya ce: “Baya tsoron komai. Me za su yi masa? Shin EFCC ce kotun shari’a?”.

Olayinka yace babu ta yadda za’ayi EFCC su gargame komai akan manufofinsa, irin mutumin da yake so ya maida kansa bayan ya bar kujerar mulki.

KU KARANTA KUMA: An sace dabbobi 36 yayinda aka nemi wani matashin makiyayi aka rasa a Plateau

Ana sanya ran Fayose zai mika mulki ga Kayode Fayemi, wanda ya lashe zaben jihar Ekiti karkashin lemar All Progressives Congress (APC) a ranar 16 ga watan Oktoba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel