Yanzu-yanzu: Karya ne, babu sojojin da suka bace – Hukumar Soji ta karyata rahoton batan dabo

Yanzu-yanzu: Karya ne, babu sojojin da suka bace – Hukumar Soji ta karyata rahoton batan dabo

Hukumar sojin Najeriya ta karyata rahoton da ke yawo a kafafan yada labarai daga jiya cewa yan tada kayar bayan Boko Haram sun kai mumunan hari barikin soji inda soji 23 sukayi batan dabo kuma an tafi da motocinsu 8.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafin ra’ayi da sada zumunta na Tuwita cewa wannan rahoto bogi ne kuma an zuzuta adadin bal jami’an sojin sun hallaka yan Boko Haram 22.

Jawabin yace: “Wannan rahoto yaudarar mutane ne kuma ba gaskiya bane. Gaskiyane yan Boko Haram sunyi kokarin sace motocin hukuma amma basu samu daman yin hakan sakamakon jaruntar sojinmi.

“Kana an hallaka yan Boko Haram 22 kuma wasu sun tsira da ciwuwwukan harsasai.”

KU KARANTA: Jami’in Kwastam ya hallaka abokan aikinsa 2 a Legas

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Al'amarin ya faru ne da safiyar ranar asabar wanda a yanzu haka manyan jami'ai guda biyar, da sojoji 18 suka bace, sai kuma manyan motoci guda 8 da suma ba a san inda suka shiga ba.

Rahoton ya nuna cewa ‘yan tada kayar bayan suna daga cikin wadanda ake zaton sun samu nasarar tserewa jami'an sojin a wani sumame da suka kai musu a baya cikin dajin sambisa da kuma tsibirin Chadi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel