El-Rufai ya maida martani ga ficewar Shehu Sani, Hukunyi daga APC tare da ayoyin al-Qur’ani

El-Rufai ya maida martani ga ficewar Shehu Sani, Hukunyi daga APC tare da ayoyin al-Qur’ani

Gwamna Nasir El-Rufai ya yi martani ga rahoton ficewar Sanata Suleiman Hunkuyi da Shehu Sani daga jam’iyyar APC mai mulki.

Gwamnan yayi martani da ayoyin al-Qur’ani kai tsaye ga yan majalisan tarayyan.

A wani rubutu da gwamnan ya wallafa a ranar Litinin mai taken rubutun hikima: “Idan alkhairi ya taba ka, yana damun su, amma idan sharri ya taba ka, sai suyi murna akai. Sannan idan kayi hakuri tare da tsoron Allah, makircin su ba zai cutar da kai ba ko kadan, Allah na kewaye da abun da suke aikatawa.” Qurani mai tsarki - Surah Aali Imraan (3:120).

El-Rufai ya maida martani ga ficewar Shehu Sani, Hukunyi daga APC tare da ayoyin al-Qur’ani

El-Rufai ya maida martani ga ficewar Shehu Sani, Hukunyi daga APC tare da ayoyin al-Qur’ani

Gwamna El-Rufai ya kuma yi amfani da hotunan sanatocin tare da rubutun.

KU KARANTA KUMA: An sace dabbobi 36 yayinda aka nemi wani matashin makiyayi aka rasa a Plateau

A wani lamari makamancin wannan, a ranar Juma’a, 11 ga watan Mayu, El-Rufai ya tsinewa sanatocin inda ya bayyana su a matysayin makiyan mutanen jihar Kaduna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel