Jami’in Kwastam ya hallaka abokan aikinsa 2 a Legas

Jami’in Kwastam ya hallaka abokan aikinsa 2 a Legas

- Tsautsayi, jami'in kwastam ya kashe abokan aikinsa biyu

-Yayinda aka ajiyesu a dakin gawawwaki, an ajiyeshi inda yeke asibiti

Jami’an hukumar Kwastam biyu sun rigamu gidan gaskiya a titin Legas-Badagry a wani mumunan hadari da ya faru ranan Asabar, 14 ga watan Yuli, 2018.

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa mutane biyu da suka rasa rayukansu sun kasance cikin mota ne kirar Toyota Camry mai lamba YLA 121 BJ, inda wani abokin aikinsu mai tuka mota kirar Toyota Avalon ya rubza cikinsu.

Jami’in Kwastam ya hallaka abokan aikinsa 2 a Legas

Jami’in Kwastam ya hallaka abokan aikinsa 2 a Legas

Yayinda jami’an biyu suka rasa rayukansu a take, shi kuma dayan jami’in na asibitin Badagry inda yake jinya.

Jami’an hukumar tsaron hanyoy FRSC karkashin jagorancin kwamanda Fatai Bakare, sun ajiye gawawwakin jami’an a dakin ajiye gawawwakin asibitin Badagry.

KU KARANTA: Sama da mutane 1,500 suka canja sheka daga PDP suka koma APC

Yace: “ Hadarin ya faru ne misalin karfe 7:45 na safiyar ranan Asabar a shataletalen Gbaji. Wani mota Toyota da jami’an kwastam ke tuakwa ya hallaka wasu jami’ai 2 abokan aikinsa.”

“Motarsa ya nufi gadar Gbaji ne yayinda tayan motan daya ya fashe.”

Hukumar FRCS sun siffanta wannan hadari a matsayin sakaci da gudun wuce gona da iri.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel