Da dumin sa: An kara samun dan takarar Shugaban kasar Najeriya a zaben 2019

Da dumin sa: An kara samun dan takarar Shugaban kasar Najeriya a zaben 2019

Wani babban malamin addinin Kirista a Najeriya kuma shugaban rukunin majami'un 'Household of God Church' mai suna Rabaran Chris Okotie a ranar Lahadin da ta gaba ta bayyana kudurin sa na sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan a zaben 2019 mai zuwa.

Babban malamin, wanda a shekarun baya na 2003, 2007 da kuma 2011 duk na nemi yin takarar shugabancin kasar amma bai samu nasara ba ya sake bayyana kudurin nasa ne a garin Legas a majami'ar sa gaban magoya bayan sa.

Da dumin sa: An kara samun dan takarar Shugaban kasar Najeriya a zaben 2019

Da dumin sa: An kara samun dan takarar Shugaban kasar Najeriya a zaben 2019

KU KARANTA: Shugabannin kasashe 10 da suka fi arziki a duniya

Legit.ng ta samu cewa Rabaran Chirs ya bayyana cewa ya fito neman zama shugaban kasar ne saboda yadda yace baya jin dadin yadda ake tafiyar da mulkin kasar musamman ma rashin tsaron da ya mamaye ko ina.

Haka ma kuma ya bayyana cewa shi yana da yakinin cewa gyaruwar Najeriya tana a hannun wasu yan kasar ne daban ba wai jam'iyyar APC ko PDP ba domin sun tun yan kasar sun ga kamun rudayin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel