APC ta bukaci Saraki ya bayyanawa al'umma jam'iyyar da yake

APC ta bukaci Saraki ya bayyanawa al'umma jam'iyyar da yake

A jiya ne Mataimakin Sakataren Jam'iyyar All Progressive Change (APC), Yekini Nabena, ya bukaci da shugaban majalisar dattawa na kasa Sanata Bukola Saraki, da ya fito ya fadawa duniya inda yasa gaba

APC ta bukaci Saraki ya bayyanawa al'umma jam'iyyar da yake

APC ta bukaci Saraki ya bayyanawa al'umma jam'iyyar da yake

A jiya ne Mataimakin Sakataren Jam'iyyar All Progressive Change (APC), Yekini Nabena, ya bukaci da shugaban majalisar dattawa na kasa Sanata Bukola Saraki, da ya fito ya fadawa duniya inda yasa gaba, ya bukaci ya fito ya tabbatar wa da al'ummar idan har yanzu yana cikin jam'iyyar APC ne ko ya koma wata jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Sama da mutane 1,500 suka canja sheka daga PDP suka koma APC

Nabena yace bukatar hakan ta taso ne ganin yanda makusanta a gareshi irin su, Alhaji Abubakar Kawu Baraje da kuma Dr. Hakeem Baba Ahmed suka bar jam'iyyar ta APC.

"Ba sau daya ba, an sha kawo suka akan irin yanda jam'iyyar APC ke gabatar da mulkinta musamman ma daga jam'iyyun adawa. Amma bamu taba ji shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki ya fito yayi Allah wadai da irin wannan suka da ake kawo jam'iyyar APC ba, bayan kuma jam'iyyar APC ita ce tayi uwa tayi uba wurin ganin ya samu mukamin da yake kai a yanzu."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel