Badakalar NYSC: Fadar Shugaban kasa ta sa a binciki Adeosun

Badakalar NYSC: Fadar Shugaban kasa ta sa a binciki Adeosun

- Fadar Shugaban kasa ta nemi a bincki Ministar kudin Najeriya

- Ana dai zargin Ministar da amfani da satifiket din NYSC na bogi

- Wasu tuni sun fara kira a tsige Ministar kudin daga mukamin ta

Mun samu labari cewa ce-ce-ku-ce da batun satifiket din Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun ya jawo ta sa Fadar Shugaban kasa ta saduda ta nemi a binciki zargin da ke kan Ministar.

Badakalar NYSC: Fadar Shugaban kasa ta sa a binciki Adeosun

Shugaban kasa Buhari yace a binciki zargin da ke kan Adeosun

Jaridar Daily Trust ta tabbatar da cewa yanzu Shugaban kasa Buhari ya ba Hukuma NYSC umarni ta binciki zargin da ke kan wuyar Ministar kudin. A baya dai Gwamnatin Buhari tayi shiru bat ace uffan game da zargin ba.

Ba mamaki ganin yadda ‘Yan adawa ke nema su jefa Ministar da kuma Gwamnatin Buhari cikin matsala ta sa Fadar shugaban kasar tayi gaggawan bada umarni a binciki gaskiyar lamarin. Zargin da ke kan Ministar yana da karfi.

KU KARANTA:

A 2002 ne Misis Kemi Adeosun ta dawo Najeriya bayan ta yi aiki a Kasar Turai, ana zargin a wancan lokaci ta nemi a ba ta takardar shaidar tsallake hidimar kasa, sai dai kuma akwai kishin-kishin din cewa ba ta samu shaidar ba.

A nan ne ake zargin Kemi Adeosun ta kirkiri shaidar bogi wanda ta rika amfani da shi. Hukumar NYSC dai tace za ta duba lamarin amma har yanzu ba ta kara cewa komai ba, har lokacin da Ministan kasar ya tuntubi Shugaban na ta.

Kwanaki kun samu labari cewa wani tsohon Jami’in Hukumar bauta na kasa watau NYSC Anthony Ani ya tabbatar mana da cewa satifiket din bogi ne a hannun Ministar kudin Najeriyar Kemi Adeosun.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel