Wasu alkawurra da sabon Gwamnan Ekiti ya yiwa al'ummar jihar

Wasu alkawurra da sabon Gwamnan Ekiti ya yiwa al'ummar jihar

Sabon zababben gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi, ya sanar da al'ummar jihar cewar zai biya su albashin da suke bin jihar a cikin farkon watanni shidan da zai iya akan aiki

Wasu alkawurra da sabon Gwamnan Ekiti ya yiwa al'ummar jihar

Wasu alkawurra da sabon Gwamnan Ekiti ya yiwa al'ummar jihar

Sabon zababben gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi, ya sanar da al'ummar jihar cewar zai biya su albashin da suke bin jihar a cikin farkon watanni shidan da zai iya akan aiki. Fayemi wanda ya fito takarar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya doke Kolapo Olusola wanda ya fito a karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda ya samu goyon bayan tsohon gwamnan jihar Ayodele Fayose.

A lokacin da yake bayani a gidan sa dake Isan-Ekiti, tsohon ministan albarkatun kasa, yace jihar ta Ekiti ta zamo koma baya a karkashin mulkin tsohon gwamnan jihar Fayose, sannan yayi wa al'ummar jihar bayar da ilimi kyauta ga dalibai.

DUBA WANNAN: Fayose ya banu: Amina ta INEC ta bukaci Fayose ya nemi afuwarta a rubuce ko tam aka shi a kotu

Ya ce, "Mutanen jihar Ekiti su saka ran samun muhimman ayyuka guda takwas. Sannan kowa ya saka ran samun albashin sa da yake bi a cikin farkon watanni shida da zanyi akan mulki. Zamu gabatar da tsarin bada ilimi kyauta ga dalibai, a ciki har da biyan kudin jarrabawar gama makarantar Sakandare ta WAEC, NECO, da kuma NABTEB.

"Zamu kara gabatar da tsari akan harkar tsaro, zamu gabatar da tsarin bayar da aikin yi ga matasa. Gwamnatin data gabata bata damu da cigaban matasan mu ba, babban burin ta shine tayi amfani dasu wurin mai dasu 'yan bangar siyasa. Saboda haka matasan mu su kwana da zummar hakan yazo karshe."

A karshe, jigo a jam'iyyar APC, Prince Dayo Adeyeye, ya nuna farin cikin sa ga irin nasarar da ya samu na lashe zaben gwamnan jihar. Inda ya kara da cewa nasarar da Fayemi ya samu zata kawo canji sosai a jihar ta Ekiti, inda yace al'ummar jihar Ekiti dama sun jima suna bukatar gwamna wanda yasan mai yake yi, wanda kuma koda yaushe yake a shirye yaga ya kawo cigaba ga al'ummar sa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel