Atiku ya nemi Magoya bayan PDP su hada-kai bayan shan kasa a zaben Ekiti

Atiku ya nemi Magoya bayan PDP su hada-kai bayan shan kasa a zaben Ekiti

- Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku yayi kira ga ‘Yan PDP

- Atiku Abubakar ya nemi Magoya bayan su ta su hada kai a Ekiti

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar nan Atiku Abubakar yayi kira ga Magoya bayan Jam’iyyar adawa a kasar nan PDP su kwantar da hankalin su duk da shan kayin da su kayi a zaben Ekiti kwanan nan.

Atiku ya nemi Magoya bayan PDP su hada-kai bayan shan kasa a zaben Ekiti

Atiku ya nemi Magoya bayan PDP su hada-kai bayan shan kasa a zaben Ekiti

Jam’iyyar ta PDP dai ta rasa Jihar Ekiti da ta ke ji da ita a zaben da ya gabata a karshen makon can. Jam'iyyar PDP ta sha kasa ne a hannun ‘Dan takarar Jam’iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar watau Dr. Kayode Fayemi.

KU KARANTA: Abin da ya sa PDP ta sha kasa a zaben Ekiti - Buhari

Sai dai babban ‘Dan siyasar Atiku ya nemi Masoya PDP su guji tada wata hatsaniya inda ya nemi Magoya bayan na su da su hada kai a Jam’iyyar. Atiku Abubakar yace PDP za ta dauki matakin da ya dace game da zaben da aka yi.

Bayan nan kuma ‘Dan takarar Shugaban kasar ya nemi Magoya bayan Jam’iyyar su fawwalawa shugabannin su komai, ka da su dauki mataki a hannun su. Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya bayyana wannan ne a Tuwita.

Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar yace zai yi bakin kokarin sa na ba manyan Jam’iyyar duk wani goyon baya da ake bukata. Jam’iyyar PDP da ‘Dan takarar ta duk sun ce ba su amince da sakamakon zaben da aka yi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel