2019: Atiku ya yiwa masu fafutukar ‘yancin Biafra wani babban alkawari matukar ya zama shugaban kasa

2019: Atiku ya yiwa masu fafutukar ‘yancin Biafra wani babban alkawari matukar ya zama shugaban kasa

- A cigaba da neman amincewa masu jefa kuri'a, jirgin Atiku ya kai bara kudancin Najeriya

- Inda roki da su ba shi laminin kuri'arsu idan har PDP ta tsayar da shi takara a zaben 2019

- Matukar ya zama shugaban kasa zai kawo karshen matsalar nan ta 'yan IPOB

Daya daga cikin masu neman takarar shugabancin kasar nan a tutar jamiyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban Atiku Abubakar, ya yi alkawarin kawo karshen matsalar nan ta tashe-tashen hankula da kasar nan ke fama da ita ciki har da masu rigimar da masu yunkurin neman kafa yan tacciyar kasar Biafara, matukar ya kai ga nasarar zama shugaban kasa.

2019: Atiku ya yiwa masu fafutukar ‘yancin Biafra wani babban alkawari matukar ya zama shugaban kasa

2019: Atiku ya yiwa masu fafutukar ‘yancin Biafra wani babban alkawari matukar ya zama shugaban kasa

Atiku ya bayyana cewa korafin da masu wannan kudurin suke da shi ya biyo bayan irin yadda gwamnati ta mayar da hankali wani bangaren kasar nan.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a Umuahian jihar Abia a lokacin da ya kai ziyarar neman goyon ga yan jamiyyar PDP da ke jihar.

KU KARANTA: Zaben Ekiti: Gwamna Fayose ya gaza kai bantensa a karamar hukumarsa

Ya kara da cewa yana daya daga cikin masu goyon bayan sake fasalta yadda kasar nan ta ke, domin hakan ne kawai zai magance matsalolin da ake fama da su.

"Matukar aka sake fasalta yanayin kasar nan, to babu shakka al'umma za ta amfana da tarin albarkatun da ke yankinsu. wanda hakan zai magance matsalolin da suka addabi kasar nan, ciki har da rikicin tabbatar da kasar Biafara" in ji Atiku Abubakar.

A karshe ya tabbatar da cewa sake fasalin kasar nan ne kawai hanya daya da za ta sake hada kan al'ummar kasar nan waje guda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel