Ziyarar kasar Netherland: Buhari ya sauka lafiya

Ziyarar kasar Netherland: Buhari ya sauka lafiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa kasar Netherland da misalin karfe 7:23 na yammacin Lahadi, 16 ga watan Yuli, don halartar taron Kotun Duniya, ICC, a birnin Hague na kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani daga cikin Alkalan Kotun ICC da ya fito daga Najeriya, Chile Eboe-Osuji ne ya tarbi shugaba Buhari a yayin da ya sauka filin sauka da tashin jirage na birnin Hague, tare da mataimakin shugaban Kotun ICC, Marc Perrin.

KU KARANTA: Horo mai tsanani: Babban laifin da gwamnatin PDP ta tafka ma jama’an jihar Ekiti

Ziyarar kasar Netherland: Buhari ya sauka lafiya

Ziyarar kasar Netherland: Buhari ya sauka lafiya

Sauran manyan jami’an gwamnati da suka tarbi Buhari sun hada da Ministan al’amuran kasashen wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, Jakadan kasar Najeriya a kasar Netherland, Oji Ngofa, jakadar kasar Netherland a Najeriya, Robert Petri, da kuma babban dogarin Sarkin Netherland,Laftanar kanal Veenhuijzen.

Kaakakin shugaba Buhari, Femi Adeshina ya bayyana cewa Buhari zai gabatar da jawabi a bikin cikar Kotun Duniyar shekaru 20 da amince da dokar kafata, haka zalika zai gaba da babban mai shigar da kara na kotun, Fatou Bensouda.

“Shi kadai ne shugaban kasa da Kotun Duniya ta gayyata, sakamakon yabawa da manufofin gwamnatinsa.” Inji Adesina.

A shekarar 1998 ne aka rattafa hannu akan dokar kafa Kotun Duniya a birnin Rum na kasar Italiya, amma har sai a shekarar 2002 ne aka kafa Kotun, inda Najeriya ta shiga jerin kasashen da suka yi amanna da Kotun a shekarar 2000. Najeriya ce kasa ta 39 cikin jerin kasashe 123 da suka yi amanna da Kotun.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel