Kotu ta damkawa EFCC wata makekiyar kadara

Kotu ta damkawa EFCC wata makekiyar kadara

- EFCC ta karbe ikon wani babban filin a jihar Legas

- Lauyan EFFC ne ya bukaci kotun ta ba su iko da fegen har ya zuwa sanda za'a kai ga yanke hukuncin

- Shari'ad ana yin ta ne tsakanin wasu, kafin daga bisani EFFC ta sanya kanta ciki

Wata babbar kotu mai zamanta a jihar Legas ta bayar da umarnin kwace wani makeken fili dake a yankin Lekki a birnin ikko, sannan ta mikawa hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC har ya zuwa lokacin da za’a yanke hukuncin karshe a shari’ar almundahanar da ake yi.

Kotu ta damkawa EFCC wata makekiyar kadara

Kotu ta damkawa EFCC wata makekiyar kadara

Alkalin da ya jagoranci yanke hukuncin, mai shari’a Muslim Hassan ya bayar da umarnin ne biyo bayan rokon hakan da lauyan EFCC ya gabatar.

Tun farko dai EFCC ta shiga shari’ar ne da ake yi tsakanin Akintayo Oloko, Macbosh Properties Ltd da kuma Safetrust Mortgage Bank.

Daga nan ne hukumar ta bukaci kotun da ta mallaka mata iko da filotin mai lamba ta 3, 116 wanda yake da fadin murabba’in kasa 5027.14 a yankin Lekki dai-dai Ikate Ancient City, cikin karamar hukumar Eti-Osa ta jihar Legas. A cewar lauyan EFCC Anana Nkereuwem

KU KARANTA: Kotu ta bayar da umarin garkame shuwagabannin jam'iyyar PDP 2 a gidan kurkuku

Lauyan na EFCC ya tabbatarwa da kotun cewa fegen da ake shari’ar a kansa cewa yana da alaka da hukumar, a don haka ne yake rokon kutun da ta damka musu shi har zuwa lokacin da za’a kammala shari’ar.

Jami’in hukumar mai bincike ya gabatar da shaidun da suka tababtar da alakar EFCC su filin domin kore kin amincewa da bukar da Mista Isaac Gong yayi, jami’in ya ce sun karbi korafin da wani mai suna Kunle Ogunmefun ya shigar kan wanda ake karar Safetrust Mortgage Bank bayan da suka ce zasu gina gida mai hawa uku cikin a wanni ashirin da hudu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel