Hukumar EFCC ta yi mi’ara-koma-baya game da batun kama Ayo Fayose

Hukumar EFCC ta yi mi’ara-koma-baya game da batun kama Ayo Fayose

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin azrikin kasa, EFCC ta yi amai ta lashe game da baraznar da ta yi na kama gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, a ranar Lahadi, 15 ga watan Yuli, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Hukumar EFCC ta yi wannan barazana ne a shafinta na Twitter, inda ta ce kariyar da gwamna Fayose ke da ita ta kare, tunda zai mika ragamar mulki nan bada jimawa ba, tare da sauka daga mulkin daga ranar 15 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Horo mai tsanani: Babban laifin da gwamnatin PDP ta tafka ma jama’an jihar Ekiti

Shi dai Fayose zai mika ragamar mulkin ne ga dan adawa, Kayode Fayemi, tsohon gwamnan jihar kuma tsohon ministar a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya lashe zaben ranar Asabar.

Hukumar EFCC ta yi mi’ara-koma-baya game da batun kama Ayo Fayose

Hukumar EFCC

Jim kadan bayan bayyana sakamakon zaben ne hukumar EFCC ta wallafa batun kama Fayose da misalin karfe 12:37 na rana, inda tace: “Rigar kariyar ta yage, sandan iko ya karye, zamu fara binciken badakalar kamfanin kiwon kajin na jihar Ekiti na naira biliyan 1.3, zamu hadu nan bada jimawaba.”

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar ta cire wannan magana daga shafinta zuwa karfe 3 na ranar Lahadin, sakamakon cece kucen da batun ta haifar a shafukan yanar gizo, inda ake zargin gwamnatin Buhari da son kai tare da nuna wariya a yaki da rashawa.

Sakamakon da hukumar zabe ta bayyana, jam’iyyar APC ta samu kuri’u dubu dari da casa’in da bakwai, da dari hudu da hamsin da tara (197,459), yayin da PDP mai mulki ta samun kuri’u dari da saba’in da takwas, da dari daya da ashirin da daya (178,121).

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel