Horo mai tsanani: Babban laifin da gwamnatin PDP ta tafka ma jama’an jihar Ekiti

Horo mai tsanani: Babban laifin da gwamnatin PDP ta tafka ma jama’an jihar Ekiti

Jim kadan bayan mummunar kayin da jam’iyyar PDP ta sha a zaben gwamnan jihar Ekiti da ya gudana a ranar Asabar, 14 ga watan Yuli, jaridar Premium Times ta tattauna da mazauna jihar, don jin musabbabin kayar da gwamnatin jam’iyyar PDP da suka yi.

A hirar da majiyar Legit.ng ta yi da wasu al’ummar jihar, ta binciko halin matsin rayuwa da suke ciki a jihar, tare da rashin samun albashin wata da watanni da gwamnatin PDP ta gaza biya ne ya sanyasu yanke shawarar kawar da PDP.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta fara kakkabe takardun binciken Fayose

Ministan ma’adanan kasa a gwamnatin shugaba Buhari daga jam’iyyar APC, Kayode Fayemi ne ya kayar da Kolapo Olusola na jam’iyyar PDP, wanda ya samu goyon bayan gwamnan jihar, Ayo Fayose, wanda ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnatin Buhari.

Horo mai tsanani: Babban laifin da gwamnatin PDP ta tafka ma jama’an jihar Ekiti

Fayose da Fayemi

Wani mazaunin karamar hukumar Ilupeju, Sunday Ogunbiyi ya bayyana cewa sama da watanni tara bai taba samun albashi ba, sa’annan duk alkawarin da gwamna Fayoshe ya yin a biyan ma’aikatan jihar bashin albashinsu kafin zabe, ya ci tura.

Haka zalika shi ma wani mazaunin garin Ado Ekiti, Sulaiman Ajide ya bayyana cewa jama’a na cikin wani kangi na talauci sakamakon tabarbarewar tattalin arziki a jihar Ekiti, don haka jama’a suka yi ma jam’iyyar PDP bore.

Shi kuma wani bakanike, mai suna Joseph Owolabi cewa yayi: “A zaman mulkin Fayemi na farko, ya gina hanyoyi da dama mai inganci, ya inganta sha’anin kiwon lafiya, ya tabbatar da tsaron jama’a da dukiyoyinsu, har ma yana biyan gajiyayyu albashin kudi naira dubu biya biyar duk wata, wannan ne dalilin da yasa na zabe shi.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel