Hari kan Gwamnan jihar Filato: Ba zamu lamunta ba – Inji Gwamnati

Hari kan Gwamnan jihar Filato: Ba zamu lamunta ba – Inji Gwamnati

Gwamnatin jihar Filato ta bara game da harin da wasu miyagun mutane bata gari suka kai ma gwamnan jihar, Simon Lalong a ranar Lahadi, 15 ga watan Yuli, jim kadan da barinsa sansanin yan gudun hijira dake unguwar Anguldi, a kudancin garin Jos.

Legit.ng ta ruwaito Kaakakin gwamnatin jihar, Yakubu Dati ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, yana nuna bacin ran gwamnatin, tare da yin Allah wadai da irin wannan mummunan lamari da ka iya jefa jihar cikin tashin tashina.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta fara kakkabe takardun binciken Fayose

Hari kan Gwamnan jihar Filato: Ba zamu lamunta ba – Inji Gwamnati

Motar

Dati yace miyagun mutanen sun yi ma gwamnan kwantan bauna ne a yayin da yake cikin ayarin motocinsa akan hanyarsa ta komawa fadar gwamnati, inda suka jefe shi da duwatsu, karafa, da sauran abubuwa daban daban, wanda suka lalata gilasan motoci da dama.

Sai dai Dati ya bayyana cewa wadanda manyan mutane ne a jihar suke daukar nauyin ire iren wannan hare hare, Ya danganta harin na ranar Lahadi ga wani hari da aka kai fadar gwamnatin jihar kimanin sati biyu da suka gabata, inda aka yi asarar motoci da dukiyoyo da dama.

Hari kan Gwamnan jihar Filato: Ba zamu lamunta ba – Inji Gwamnati

Motar

Sanarwar ta bada tabbacin burin gwamnatin jihar na daukar matakin da ya dace akan duk masu hannu cikin wannan hare hare, musamman duba da yadda take kan jiki kan karfi wajen shawo kan matsalar tsaro a jihar, amma wasu dake amfana da matsalar basa kaunar ganin an zauna lafiya.

Daga karshe gwamnan ya jinjina ma jami’an tsaro dake cikin ayarin gwamnan ta yadda suka nuna dattaku da kwarewa ba tare da janyo asarar rayuka ba, sa’annan yayi kira ga iyaye da su ja hankulan yayansu don kauce ma ayyukan ashsha da dana sani.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel