Motar wani Fasto ta runtuma cikin masu murnar zaben gwamnan Ekiti bayan ta kubce bisa kuskure

Motar wani Fasto ta runtuma cikin masu murnar zaben gwamnan Ekiti bayan ta kubce bisa kuskure

- Garin murna cin zaben jihar Ekiti baya ta haihu

- Wani malamin Coci ya yi sukuwar Sallah da motarsa a kan wani yaro yayin murnar zabe

- Yanzu haka dai yaron yana asibiti cikin mawuyacin hali

Da safiyar yau ne wata karamar mota da wani Fasto ke tukawa tayi cikin mutane wadanda su ke tsaka da murnar lashe zaben gwamnan jihar Ekiti Kayode Fahemi ya yi, inda ta yi sukuwar Sallah da wani yaro dan kimanin shekaru 7 mummunan rauni.

Motar wani Fasto ta runtuma cikin masu murnar zaben gwamnan Ekiti bayan ta kubce bisa kuskure

Motar wani Fasto ta runtuma cikin masu murnar zaben gwamnan Ekiti bayan ta kubce bisa kuskure

Bayanin likitoci ya nuna cewa yaron yana cikin mawuyacin hali, a don haka ne suka bukaci iyayensa su dage da yi masa addua.

Wani da abin ya faru akan idonsa ya bayyana cewa deriban malamin Coci ne, kuma lamarin ya faru ne a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa ibada a cocin da ya ke bauta.

KU KARANTA: Abinda na fadawa shugabannin PDP da suka ziyarce ni jiya – Obasanjo

Tun da farko dai an garzaya da yaron mai suna Imole Afolabi, zuwa wani Asibiti domin ceton rayuwarsa, amma daga bisani jami'an asibitin suka rufe shi domin yawaitar hargowar jama'a.

Mahaifiyar yaron mai suna Funmilola ta bayyana cewa ta shiga jerin makota ne domin nuna murnarsu bisa nasarar lashe zaben da Kayode Fayemi yayi, inda su ka taru akan shatale-talen Ilupeju.

Faruwar hakan ke da wuya sai mahaifiyar yaron wacce ta ke sanye da rigar dan takarar da ya yi nasara ta yanke jiki ta fadi.

A nasa bangaren kuwa, malamin Cocin ya bayyana cewa al'amarin tsautsayi ne kawai, domin ba gudu ya ke na wuce ka'ida ba. Sannan ya bayyana jimaminsa bisa faruwar hadarin tare kuma da yin addu'ar Allah ya baiwa majiyyacin lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel