Dalilin da yasa Fayose da PDP suka fadi zabe a Ekiti – Fadar shugaban kasa

Dalilin da yasa Fayose da PDP suka fadi zabe a Ekiti – Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da take gani shine silar nasarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Ekiti da aka yi jiya, Asabar, 14 ga watan Yuli.

A jawabin da Garba Shehu, kakakin shugaba Buhari ya fitar a yau, Lahadi, ya bayyana cewar nasarar jam’iyyar APC alama ce dake nuna cewar mutanen jihar Ekiti sun amince da gwamnatin shugaba Buhari.

Yakin shugaba Buhari a kan cin hanci da rashawa da aiyukan ta’addanci, kokarinsa a kan harkar nomad a aiyukan raya kasa, rikon amanar dukiyar kasa da rabon arzikin kasa ga kowacce jiha ba tare da nuna banbancin siyasa ba, sune abubuwan da suka bawa mutanen Ekiti karfin gwuiwar zaben APC duk da irin karya da bata suna da Fayose ya yi masa a jihar,” a cewar Garba Shehu.

Dalilin da yasa Fayose da PDP suka fadi zabe a Ekiti – Fadar shugaban kasa

Dalilin da yasa Fayose da PDP suka fadi zabe a Ekiti – Fadar shugaban kasa

Saidai jam’iyyar PDP tayi watsi da sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar na zaben gwamnan jihar Ekiti da aka yi jiya.

DUBA WANNAN: Abinda na fadawa shugabannin PDP da suka ziyarce ni jiya – Obasanjo

A sakamakon da INEC ta fitar, dan takarar jam’iyyar APC, Kayode Fayemi, ya sami nasara a kan dan takarar PDP, Farfesa Kolapo Olusola.

Da sanyin safiyar yau, Lahadi, ne hukumar INEC ta sanar da cewar Fayemi na APC ya samu nasara a kananan hukumomi 11 a cikin 16 dake jihar ta Ekiti. Fayemi ya samu jimillar kuri’u 197,459 yayinda Kolapo ya samu kuri’u 178,121.

A jawabin da ta fitar ta bakin kakakinta, Kola Ologbondian, ta bayyana cewar an yi masu fashin zabe da tsakar rana tare da yin watsi da sakamakon zaben gabadayansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel