Fayose ya banu: Amina ta INEC ta bukaci Fayose ya nemi afuwarta a rubuce ko tam aka shi a kotu

Fayose ya banu: Amina ta INEC ta bukaci Fayose ya nemi afuwarta a rubuce ko tam aka shi a kotu

Amina Zakari, kwamishiniya a hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta nemi gwamnan jihar Ekiti mai baring ado, Ayodele Fayose, day a rubuto mata takardar neman afuwa tare da janye kalaman day a yi a kanta ko kuma ta maka shi a kotu.

A wata wasika da ta aikewa Fayose ta hannun lauyanta, Ubong Akpan, Amina ta bayyana cewar zata garzaya kotu domin neman hakkinta a kan illar da Fayose ya yiwa lafiyarta, aikinta da kuma mutuncinta.

A ranar 2 ga watan Yuli ne, Fayose ya zargi Amina da yin aiki tare da jam’iyyar APC domin kayar da jam’iyyarsa ta PDP a zaben gwamnan jihar da aka kamala jiya, Asabar, 14 ga watan Yuli.

Fayose ya banu: Aisha ta INEC ta bukaci Fayose ya nemi afuwarta a rubuce ko tam aka shi a kotu

Aisha Zakari da Fayose

Kazalika ya zargi hukumomin tsaro na ‘yan sanda da DSS da canja masu tsaron lafiyar Fayemi domin samun dammar yin magudi a zaben da jam’iyyar PDP ta sha kaye.

DUBA WANNAN: PDP tayi watsi da sakamakon zaben Ekiti, duba hotunan da ta saki a matsayin shaidar magudi

Amina, ta hannun lauya, Akpan t ace ta bawa Fayose kwanaki biyu kacal ya rubuta takardar neman afuwarta da za a buga a manyan jaridun kasar nan ko kuma su hadu a kotu.

Tuni dai rahotanni suka bayyana cewar hukumar EFCC ta sanar da Fayose cewar tana jiransa domin gurfanar da shi a kotu tunda yanzu ya fadi zabe, kariyar da yake da ita ta kare.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel