Da duminsa: Shugaba Buhari ya shilla zuwa kasar Holland, duba hotuna

Da duminsa: Shugaba Buhari ya shilla zuwa kasar Holland, duba hotuna

Bayan dawowarsa daga kasar Mauritania, Shugaba Muhammadu Buhari yanzu haka na kan hanyarsa ta zuwa kasar Netherland a nahiyar Turai domin halartan taron murnan zagayowar ranan amincewa da amfani da dokar Roma a matsayin kundin babban kotun duniya dake hukunta laifukan ta'addanci( ICC).

Legit.ng ta samu wannan labari ne a wani jawabi da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya saki a jiya Asabar.

Garba Shehu ya bayyana cewa : "Shugaba Buhari zai tafi ranar Lahadi, 15 ga watan Yuli 2018 inda zai gabatar da jawabi a babban kotun.

Da duminsa: Shugaba Buhari ya shilla zuwa kasar Holland, duba hotuna

Shugaba Buhari kafin tashinsa

Da duminsa: Shugaba Buhari ya shilla zuwa kasar Holland, duba hotuna

Shugaba Buhari ke dagawa jama'a hannu kafin shiga jirgi

A cewar Garba Shehu, Buhari kadai ne shugaban kasa a duniya da zai gabatar da jawabi a taron.

Bayan taron, shugaba Buhari zai tattauna da babban lauyan kotun ICC, Ms Fatou Bensouda, kana zai gana da alkalin alkalan kotun, Chile Eboe-Osuji, wanda asalinsa dan Najeriya ne.

DUBA WANNAN: Abu 4 da PDP zata yi domin dawo da martabarta a Najeriya - Obasanjo

Bugu da kari, shugaba Buhai zai gana Firam Ministan Holland, Mart Ruttr, domin tattaunawan diflomasiyya kuma zasu rattaba hannu kan wasu yarjejeniya.

Wadanda za su raka shugaba Buhari sune gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong; gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu; karamar mininstan masana'antu, Aisha Abubakar; ministan harkokin wajen Najeriya, Geofrey Onyeama; da ministan Shari'a, Abubakar Malami. Sauran Sune minisatan noma, Audu Ogbeh; Shugaban kamfanin NNPC, Maikanti Baru; shugabar hukumar kula da tashar jiragen ruwa ta kasa, Hadiza Bala Usman.

Da duminsa: Shugaba Buhari ya shilla zuwa kasar Holland, duba hotuna

Shugaba Buhari zaune, bayan ya samu natsuwa, a cikin jirgin shugaban kasa
Source: Twitter

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel