Hukumar EFCC ta fara kakkabe takardun binciken Fayose

Hukumar EFCC ta fara kakkabe takardun binciken Fayose

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC za ta taso Gwamnan Ekiti Ayo Fayose a gaba. Hukumar ta EFCC ta fara kakkabe takardun ta domin fara binciken badakalar da ke kan Fayose.

EFCC na zargin Fayose da laifuffuka da dama

Dazu ne dai Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin kasa barna ta tabbatar da cewa watan damke Gwamna Ayodele Fayose ya kusa kankama. Ana zargin Gwamnan da karkatar da kudin Jihar sa wajen gina gidan gona.

EFCC dai tana jira ne kurum Gwamnan ya sauka daga kujerar sa ta yi ram da shi. Dokar kasa ba ta bada dama a bincike Gwamna da Shugaban kasa ba muddin su na kan mulki. Kwanan nan ne Fayosen zai mika mulkin Jihar.

KU KARANTA:

Mun ma ji kishin-kishin din cewa Gwamnan mai shirin ajiye ragamar mulki ya fara shirin barin Najeriya. Ana rade-radin cewa tuni har Gwamnan yayi fasfo ya kuma saye tikitin jirgi domin tserewa daga Najeriya kwanan nan.

EFCC tayi wannan jawabi ne ta shafin ta na Tuwita inda ta ce ta na sa ran haduwa da Gwamnan kwanan nan. A jiya ne ‘Dan takarar Jam’iyyar APC Kayode Fayemi ya doke Jam’iyyar PDP ta su Fayose ya lashe kujerar Gwamnan Jihar.

Dazu kun ji cewa Gwamna Ayo Fayose ya koka da yadda aka gudanar da zaben Gwamnan Jihar Ekiti. Ayo Fayose da ke shirin ajiye mulki ya zargi ‘Yan Sanda da murde zaben Gwamnan Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel