Abinda na fadawa shugabannin PDP da suka ziyarce ni jiya – Obasanjo

Abinda na fadawa shugabannin PDP da suka ziyarce ni jiya – Obasanjo

A jiya ne shugabancin jam’iyyar PDP karkashin jagorancin shugabancinta na kasa, Uche Secondus, suka ziyarci tsohon shugaban kasa Obasanjo. Bayan ziyarar tasu, Ofishin yada labarai na Obasanjo ya aike da jawabin yadda ganawar ta su ta kasance.

Bayan ya yi masa godiya bisa ziyartar shi tare da neman afuwarsa bisa kuskuren day a saka shi ficewa daga jam’iyyar, Obasanjo ya zayyana wasu abubuwa hudu da dole PDP ta mallake su muddin tana bukatar mulkin Najeriya ya dawo hannunta. Abubuwan da Obasanjo ya lissafa sune; da’a, himma, shugabancin nagari da kuma tsayar da nagartattun ‘yan takara.

Abinda na fadawa shugabannin PDP da suka ziyarce ni jiya – Obasanjo

Shugabannin PDP da Obasanjo

Obasanjo ya shaidawa shugabannin PDP cewar bashi da sha’awar komawa cikin jam’iyyar amma kuma a shirye yake ya hada gwuiwa da duk masu son kawowa Najeriya cigaba kuma hakan ne ma ya saka shi shiga Hadaka da wasu jam’iyyu kafin daga bisani ya yanke shawarar kafa jam’iyyar ADC.

DUBA WANNAN: Zaben Ekiti: Buhari ya taya Fayemi murna, ya yi masa hudubar girma

Tsohon shugaba Obasanjo ya kara cewa zai cigaba da kasancewa cikin shiri domin bayar da gudunmawa ga kungiyoyin maza da mata ko jam’iyyu domin ceto Najeriya daga halin da take ciki a karkashin mulkin APC.

Obasanjo ya fice ne daga PDP gabanin zaben 2015 bayan ya zargi jam’iyyar da Jonathan, shugaban kasa na wancan lokacin, da gazawa wajen warware matsalolin da Najeriya ke fama da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel