Dawo-dawo: Mutanen Ekiti sun yi murna bayan Fayemi ya lashe zaben Gwamna

Dawo-dawo: Mutanen Ekiti sun yi murna bayan Fayemi ya lashe zaben Gwamna

- INEC ta tabbatar da Fayemi zai zama sabon Gwamna Jihar Ekiti

- An yi murna da aka ji ‘Dan takarar na Jam’iyyar APC yayi nasara

- Jama’a sun yi farin cikin jin Jam’iyyar PDP ta rasa mulkin Jihar

Dazu labari ya zo mana cewa tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi ya lashe zaben da aka gudanar a Jihar Ekiti inda ya samu nasara kusan a duka Kananan Hukumomin Jihar face guda 3.

Dawo-dawo: Mutanen Ekiti sun yi murna bayan Fayemi ya lashe zaben Gwamna

Jama'a wajen murna bayan Fayemi ya ci zaben Gwamna

Mutanen Gari sun fito sun nuna farin cikin su da jin cewa tsohon Gwamnan ne yayi nasara a zaben da aka yi jiya. Tsohon Ministan na Shugaba Buhari ya samu kuri’a sama da 197, 000 inda ya doke ‘Dan takarar Jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Sarki goma zamani goma: An yi sabon Gwamna a Jihar Ekiti

Dawo-dawo: Mutanen Ekiti sun yi murna bayan Fayemi ya lashe zaben Gwamna

Magoya bayan APC a cikin Garin Ado-Ekiti su na murna dazu

Jama’a sun nuna murnar su a fili inda su ka fito kan titi a cikin babban Birnin Ado-Ekiti su na wasa da motoci da Babura. Magoya bayan Kayode Fayemi sun ji dadin yadda Mataimakin Gwamnan Ayo Fayose ya sha kasa a zaben Jihar.

Tuni dai aka fara taya sabon Gwamnan murna na komawa kujerar sa da ya rasa a 2014 wajen Ayo Fayose. Gwamn Ayo Fayose wanda ke shirin barin gado ya koka da yadda aka yi amfani da Jami’an tsaro wajen murde zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel