Ayo Fayose ya zargi ‘Yan Sanda da murde zaben Jihar Ekiti

Ayo Fayose ya zargi ‘Yan Sanda da murde zaben Jihar Ekiti

- Gwamna Ayo Fayose ya koka da yadda aka gudanar da zaben Ekiti

- ‘Dan takarar Jam’iyyar APC Kayode Fayemi ya doke Jam’iyyar PDP

Labari ya zo mana cewa Gwamn Ayo Fayose wanda ke shirin barin gado ya koka da yadda aka yi amfani da Jami’an tsaro wajen murde zaben. Gwamnan yayi wannan bayani ne a jiya lokacin da yayi zabe a Garin Afao da ke Ekiti.

Ayo Fayose ya zargi ‘Yan Sanda da murde zaben Jihar Ekiti

Fayose yace Jami'an tsaro su ka murde zaben Ekiti

Gwamna Fayose ya koka game da yadda aka gudanar da zaben Jihar Ekiti inda yace abin kunya ne a kasar gaba daya. Gwamnan da ke shirin barin kujerar say ace an yi amfani da ‘Yam Sanda wajen tada rikici a wurin zaben.

KU KARANTA: Zaben Ekiti: Buhari ya taya Fayemi murna, ya yi masa hudubar girma

Ayo Fayose ya bayyana cewa ‘Yan Sanda sun kama mutanen sa da-dama sun daure. Daga cikin wadanda'Yan Sanda su ka yi ram da su akwai Shugaban Ma’aikatan gidan Gwamnatin Jihar Ekiti inji Mai Girma Gwamna Ayo Fayose.

Fayose ya bayyanawa ‘Yan Jarida cewa yayi kokarin kiran Jami’an tsaro a wayar salula amma bas su daukar wayar sa. Gwamnan yace ‘Yan Sanda sun karbe aikin Jami’an Hukumar zabe na INEC inda su ka rika satar akwatin zabe.

Gwamnan ya bayyana cewa an sace akwatunan zabe a Garin Ado da kuma Garin Ikere watau Garin ‘Dan takarar PDP. ‘Dan takarar PDP watau Farfesa Olusola Eleka ya bayyana cewa Jami’an tsaro sun hada baki da APC su na murde zaben

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel