Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun yi tsokaci game da sakamakon zaben jihar Ekiti

Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun yi tsokaci game da sakamakon zaben jihar Ekiti

Wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki da suka hada da Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-rufai da kuma Orji Uzur Kalu sun tofa albarkacin bakin su game da sakamakon zaben gwamnan jihar Ekiti da ya gudana a jiya.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa dai ta ayyana tsohon gwamnan jihar kuma tsohon ministan albarkatun kasa, Kayode Fayemi a matsayin wanda yayi nasarara a zaben.

Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun yi tsokaci game da sakamakon zaben jihar Ekiti

Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun yi tsokaci game da sakamakon zaben jihar Ekiti

KU KARANTA: Bayan faduwa zabe, za'a maka Fayose kotu

Legit.ng ta samu cewa da yake nashi tsokacin, Gwamna Nasiru El-rufai ya taya shi murna tare da dukkan 'yan jihar dama jam'iyyar su a kasa baki daya. Gwamnan ya kuma yabawa shugaban gangamin yakin neman zaben a jihar kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu da samun nasara.

Haka ma shima Cif Orji Kalu ya taya sabon zababben gwamnan jihar akan nasarar da ya samu tare da dukkan daukacin kabilar yarbawa da suka kara samun nasara.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel