Mafusatan matasa sun yi wa ayarin wani gwamnan Arewa ruwan duwatsu

Mafusatan matasa sun yi wa ayarin wani gwamnan Arewa ruwan duwatsu

Wasu matasa da ake zargin masu zaman banza ne a jiya sun yiwa ayarin gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong ruwan duwatsu akan hanyar sa ta komawa Jos, babban birnin jihar bayan ya kai ziyara wani sansanin 'yan gudun hijira.

Majiyar mu dai a samu cewa a cikin ayarin gwamnan da matasan suka jefa hadda mataimakin sa Farfesa Sonni Tyoden, da sakataren gwamnatin jihar Rufus Bature dama wasu mutanen da dama.

Mafusatan matasa sun yi wa ayarin wani gwamnan Arewa ruwan duwatsu

Mafusatan matasa sun yi wa ayarin wani gwamnan Arewa ruwan duwatsu

KU KARANTA: Yadda wata ta yanke azzakarin mijin ta saboda kishi

Legit.ng ta samu sai dai wasu jami'an gwamnatin jihar sun yi zargin cewa matasan 'yan siyasa ne suka sa su ci mutuncin gwamnan kuma sannan za su yi bincike su kuma hukunta duk wani mai hannu a ciki.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin manyan jami'an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa National Electoral Commission, INEC kuma kwamishinar da ke kula da harkokin zabe da tafiyar da ayyuka Hajiya Aminat Zakari ta ba gwamnan jihar Ekiti mai barin gado kwana biyu ya bata hakuri ko kuma su hadu kotu.

Kwamishinar dai ta ba shi wa'adin ne biyo bayan zargin da yayi mata tare da wasu mutanen da jami'an tsaro ta hada baki da 'yan siyasa a jihar wajen murde zaben da aka gudanar na gwamna a jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel