Ta faru ta kare: Kayode Fayemi ya sake zama Gwamnan Jihar Ekiti

Ta faru ta kare: Kayode Fayemi ya sake zama Gwamnan Jihar Ekiti

- Kayode Fayemi ya sake zama Gwamnan Jihar Ekiti bayan ya sha kashi a 2014

- Jam’iyyar APC ce ta doke PDP ta karbe mulki daga hannun su Fayose a zaben

Mun samu labari cewa tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Dr, Kayode Fayemi ya sake zama Gwamnan Jihar bayan ya lashe zaben da aka yi jiya. Fayemi ya tika ‘Dan takarar Gwamna mai-barin gado Fayose ne da kasa duk da an yi zargin amfani da kudi.

Ta faru ta kare: Kayode Fayemi ya sake zama Gwamnan Jihar Ekiti

Kayode Fayemi ya lashe zaben Gwamnan Jihar Ekiti

Tsohon Ministan Ma’adanai na Gwamnatin Shugaba Buhari watau Dr. Kayode Fayemi ya doke ‘Dan takarar PDP Farfesa Olusola Eleka a zaben sabon Gwamnan Jihar Ekiti. The Nation ta rahoto cewa har Fayose ya sha kashi a Karamar Hukumar sa.

KU KARANTA: Mataimakin Fayose ya sha kashi a hannun ‘Dan takarar APC

‘Dan takarar PDP Olusola Eleka yace da Jami’an tsaro aka yi amfani aka murde zaben. Dama can kun ji cewa Mataimakin na Gwamna Ayo Fayose ya fara kuka bayan ya hango zai sha kashi a zaben a hannun ‘Dan takarar APC Dr. Kayode Fayemi.

APC tayi nasara a Kananan Hukumomin Jihar irin su: Ilejemeje, Moba, Irepodun-Ifelodun, Oye da wasu Garuruwa 8. A zaben, PDP mai rike da mukin Jihar ta iya yin nasara ne a Karamar Hukumar a Efon, Ikere da kuma babban Birnin Ado-Ekiti.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel