Zaben Ekiti: Buhari ya taya Fayemi murna, ya yi masa hudubar girma

Zaben Ekiti: Buhari ya taya Fayemi murna, ya yi masa hudubar girma

Shugaban kasa Muhammadu ya taya zababben gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, murnar lashe zaben da aka yi jiya, Asabar, 14 ga watan Yuli.

Shugaba Buhari ya jinjinawa Fayemi da ma dukkan magoya bayan jam'iyyar APC bisa jajircewar su da ta kai ga samun wannan nasara.

Buhari ya ja hankalin sabon gwamnan da ya tabbatar ya tafi da duk jama'ar jihar Ekiti a gwamnatinsa ba tare da la'akari da banbancin siyasa ba.

Zaben Ekiti: Buhari ya taya Fayemi murna, ya yi masa hudubar girma

Buhari ya taya Fayemi murna, ya yi masa hudubar girma

Kazalika ya yabawa mutanen jihar Ekiti bisa dagewar su wajen zaben sabuwar gwamnati da zata inganta rayuwar su.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ma ta sha yabo a wurin Buhari tare da yaba mata bisa yadda ta shirya zaben cikin nasara.

DUBA WANNAN: Zaben Ekiti: Kalli hotunan murnar magoya bayan Fayose bayan sun yi ikirarin hango kyallin nasara

Shugaba Buhari ya kara mika jinjina ga jami'an tsaro bisa tabbatar da tsaro yayin zaben na jiya.

Ga wadanda suka fadi zabe, shugaba Buhari ya bukaci da su zama masu hakuri da yakana sabanin kokarin kawowa gwamnati mai shigowa matsala.

"Wannan nasara ce ta mutanen jihar Ekiti da ma dimokradiyya gabadaya," a cewar shugaba Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel