Hukumar lura da kafafen yada labarai ta rufe gidan Radiyo jihar Ekiti

Hukumar lura da kafafen yada labarai ta rufe gidan Radiyo jihar Ekiti

- Bayana faduwa zaben da dan takarar da ya tsayar yayi, yanzu haka an garkame gidan Radiyon jihar Ekiti

- Da ma dai mutane da yawa sun sha sukar gwamna mai barin gadun da cewa ya fiye wuce makadi da rawa

- Ciki kuwa har da tsohon shugaban kasa Obasanjo, inda ya ce an fi jiyo amon gwamna Fayosen kan abubuwan ashararanci maimakon cigaba

Hukumar lura da kafafen yada labarai ta kasa wato NBC ta rufe gidajen radiyo da talabijin mallakar jihar Ekiti a sakamakon sanarwar da gwamnan jihar Ayodele Fayose cewa dan takarar jamiyyar PDP ne ya lashe zaben gwamnan da aka gudanar a jiya asabar din.

Hukumar tarayya ta rufe gidan Radiyo jihar Ekiti

Hukumar tarayya ta rufe gidan Radiyo jihar Ekiti

Sanarwar da gwamnan ya bayar na zuwa ne adaidai lokacin da hukumar zabe take tattara sakamakon zaben daga kananan hukumomi 16 da ke fadin jihar.

KU KARANTA: Zaben Ekiti: Gwamna Fayose ya gaza kai bantensa a karamar hukumarsa

Rahotanni sun tabbatar da cewa a lokacin da gwamnan ya bayar da sanarwar hukumar INEC ba ta kai ga bayyana wanda ya lashe zaben ba, wanda hakan ya sabawa dokokin zabe na kasa.

Hukumar tarayya ta rufe gidan Radiyo jihar Ekiti

Hukumar tarayya ta rufe gidan Radiyo jihar Ekiti

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel