Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabon zababben gwamnan jihar Ekiti

Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabon zababben gwamnan jihar Ekiti

- Takaitaccen bayani game da tsohon Ministan Buhari na da kuma zababben gwamnan Ekiti da suka kunshi karatunsa da inda ya yi aikace-aikacensa har kawo yanzu da sa sake samun nasarar zamowa gwamna

- Kafin zaben dai an kai ruwa rana kan yadda ake gani zaben zai kaya

Cikakken sunanasa shi ne John Olukayode Fayemi an haife shi a ranar 9 ga watan Fabrairu a shekarar 1965 a karamar hukumar Oye ta jihar Ekiti daga kabilar yarbawa (mazauna) Isan-Ekiti.

Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabon zababben gwamnan jihar Ekiti

Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabon zababben gwamnan jihar Ekiti

Ya halarci makarantar Christ's School Ado Ekiti domin karatun digirinsa daga 1975 zuwa 1980 a fannin tahiri da siyasa, sai kuma wasu digirorin daga jami’ar Legas da Ife duk a Najeriya, yayin da ya yi wani digirin a jami’ar Kings College dake birnin Landan a kasar Ingila.

KU KARANTA: Dawo-dawo: Fayemi ya kama hanyar zama sabon Gwamnan Jihar Ekiti

Ya kuma ajiye mukaminsa na ministan cigaban ma’adanai na kasa ranar 30 ga watan Mayu na 2018 domin samun damar tsayawa takarar gwamnan jiharsa.

Ga jadawalin mukamai da shekarar da ya rike har kawo yanzu da aka sake zabarsa a karo na biyu.

1985–1986 — Malami a makarantar horas da jami’an ‘yan sanda dake Sokoto

1987–1989 — Jami’in bincike kuma shugaban kamfanin tsare-tsare da dabarun cigaba a Legas

1992–1992 — Aiki da sashin dabarun yaki na kwalejin koyon yaki dake Landan

1991–1993 — Jami’in bincike a cibiyar tattara bayanai dake Landan

1993–1995 — Mashawarci ga Deptford City Challenge a Ingila

1995–1997 — Sakatare a Media Empowerment for Africa (The Radio Foundation)

1997–2006 — Daraktan cibiyar Dimukuradiyya da cigaba

2010–2014 — Gwamnan jihar Ekiti

2015- 2018 – Ministan cigaban ma’adanai ta kasa

Yanzu haka dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben jihar da aka gudanar a jiya Asabar, hakan na nufin burin gwamna mai barin gado Ayodele Fayose ya gaza cika kenan na dora mataimakinsa don ya maye gurbinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel