Ana kukan tsaro an aika Jami’an ‘Yan Sanda da Sojoji wajen zaben Ekiti

Ana kukan tsaro an aika Jami’an ‘Yan Sanda da Sojoji wajen zaben Ekiti

- Gwamnatin Tarayya ta aika Jami’an tsaro da dama zuwa Ekiti

- Wasu na ganin cewa an yi sakaci da harkar tsaro a wasu wurare

- Yanzu dai an kai wasu hare-hare a bangaren Arewacin Najeriya

Mun samu labari cewa wasu Jama’a sun yi tir da yadda aka baza Jami’an tsaro rututu a wajen zaben Gwamnan Jihar Ekiti yayin da ake ta kashe Bayin Allah a cikin kasar babu gaira babu dalili.

Ana kukan tsaro an aika Jami’an ‘Yan Sanda da Sojoji wajen zaben Ekiti

An jibga Jami'an tsaro na kin-karawa wajen zaben Ekiti

Wani tsohon ‘Dan Majalisar Jihar Bauchi Aliyu Ibrahim ya koka da yadda ake cigaba da mutane a Jihar Zamfara inda ya nemi a hukunta masu wannan ‘danyen aiki. Kwanan nan ne ma kuma aka hallaka mutane kusan 40 a Jihar Sokoto.

Duk da wannan dai Gwamnatin Tarayya ta tura Jami’an ‘Yan Sanda 30, 000 wajen aiki a zaben Gwamnan Jihar Ekiti. Bayan nan kuma ana rade-radin cewa an aika manyan Sojoji da kuma jiragen yaki da Jami’an fararen kaya na DSS rututu.

KU KARANTA: An sake yin wasu kashe-kashe a Arewacin Najeriya

A baya dai Jam’iyyar APC ta koka da yadda Gwamnatin Jonathan ta tura Jami’an tsaro zuwa zaben Ekiti a 2014. A lokacin Jam’iyyar adawa ta APC ta koka da cewa Gwamnati ba ta dauki matakin maganin Boko Haram ba amma tana murde zabe.

Kwanan nan ne dai aka kashe mutane da dama a wani Kauye da ake kira Tabani da ke cikin Garin Sokoto yayin da ake shirin zaben Ekiti. A lokacin zaben Gwamnan Jihar Ekiti a 2014, Gwamnati ta sha sukar gaske kan rikicin Boko Haram.

A zaben na Ekiti da aka yi a jiya, Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti kuma ‘Dan takarar APC Dr. Kayode Fayemi ne kan gaba kamar yadda Hukumar zabe na kasa watau INEC ta sanar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel