Sanata Shehu Sani ya bada mu inji Mai ba Shugaban kasa shawara

Sanata Shehu Sani ya bada mu inji Mai ba Shugaban kasa shawara

Mai ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawara a kan kafofin sadarwa na zamani Lauretta Onochie tayi tir da Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki.

Wata Hadimar Shugaban kasa ba ta ji dadin wasu jawabi da ‘Dan Majalisar na Jihar Kaduna yayi ba, dalilin haka ne Onochie tace Sanatan ya ba su kunya. Mai ba Shugaban kasar shawara tayi wannan magana ne a Ranar Juma’ar nan.

Sanata Shehu Sani ya bada mu inji Mai ba Shugaban kasa shawara

Sanata Shehu Sani ya gamu da suka daga Fadar Shugaban kasa

A shafin sa na Facebook, Sanatan ya bayyana cewa shi da ire-iren sa a Jam’iyyar APC sun zama kamar Mutanen da su ka sha wahala a hannun Fir’ana, yanzu su ke gabar babban tekun da za su tsira su huta da wahala da tsangwama a Kasar.

KU KARANTA: An samu wasu 'Yan Majalisa da laifi a Najeriya

‘Dan Majalisar dai ba mamaki yayi habaicin da ya saba ne, inda yake nuna cewa Shugaba Buhari ya tsangwame su a Jam’iyyar APC don haka za su tattara su sauya sheka. Onochie ta maida martani inda tace Sanatan ba zai kai labari ba.

Lauretta Onochie a na ta jawabin tace Sanatan da ire-iren sa ba za su sha ba, don kuwa za su fada cikin ruwa ne. Mai ba Shugaban kasa shawarar tace irin su Sanatan na Kaduna Shehu Sani sun ba APC kunya kuma ba za su kai labari ba.

Onochie ta fadi alherin wannan Gwamnatin ta Buhari da ta rika rabawa Talakawa kudi har N5000 a kowane wata na Allah a Kasar. A cewar ta abin da kurum Gwamnatin Buhari tayi la’akari da shi, shi ne talauci, ba addini ko ra’ayin siyasa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel