Tazarcen Buhari: Ba a nada Ali Modu Sheriff cikin kwamitin neman zabe ba - SGF

Tazarcen Buhari: Ba a nada Ali Modu Sheriff cikin kwamitin neman zabe ba - SGF

- Sakataren Gwamnatin Tarayya ya karyata rade-radin da ke yawo a Gari

- Da kun ji cewa an nada Ali Sheriff cikin masu nemawa Buhari goyon baya

Mun samu labari cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ya bayyana cewa ba a nada tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP Ali Modu Sheriff a matsayin Shugaban yakin neman zaben Buhari ba.

Tazarcen Buhari: Ba a nada Ali Modu Sheriff cikin kwamitin neman zabe ba - SGF

Gwamnatin Tarayya tace babu gaskiya game da kwamitin Sheriff
Source: Facebook

Sakataren na Gwamnatin Najeriya Boss ya karyata wannan magana ne ta bakin Darektan sa na yada labarai Lawrence Ojabo. A baya dai an rahoto cewa Ali Sheriff ne zai jagoranci wani kwamiti na goyon bayan Buhari a zaben 2019.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Kayode Fayemi ya lashe zaben Jihar Ekiti

Boss yace rahoton sam ba daidai bane domin takardun da aka samu wannan labari daga gare su, ba su inganta ba. ‘Daya daga cikin mai ba Shugaba Buhari shawara kan harkokin siyasa Gideon Sammani ne ya fitar da wannan sanarwa a baya.

Sakataren Gwamnatin na Tarayya dai ya nemi ayi watsi da wannan maganar na cewa an kafa wani kwamiti mai mutum 35 da za su nemawa Shugaban Kasa Buhari goyon baya a zabe mai zuwa. A jerin har da wasu ‘Yan Majalisa da Mawaka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel