An cimma yarjejeniyar yin aiki tare tsakanin Obasanjo da PDP

An cimma yarjejeniyar yin aiki tare tsakanin Obasanjo da PDP

Mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP karkashin shugabanta na kasa, Uche Secondus, sun gana da Obasanjo a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, a yau, Asabar.

Dakarun 'ya'yan PDP da suka halarci ganawar da Obasanjo sun hada da, shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar, The Walid Jubrin, Cif Bode George, da tsohon shugaban majalisar dattijai, Sanata Adolphus Wabara. Tuni dukkansu suka isa jihar Ogun tun jiya.

An cimma yarjejeniyar yin aiki tare tsakanin Obasanjo da PDP

Obasanjo da shugabannin PDP

An cimma yarjejeniyar yin aiki tare tsakanin Obasanjo da PDP

An cimma yarjejeniyar yin aiki tare tsakanin Obasanjo da PDP

Bayan wata ganawa ta tsawon sa’o’I biyu tsakanin shugabancin PDP da tsohon shugaban kasa Obasanjo, jam’iyyar, tab akin sakatarenta na yada labarai, Kola Ologbondian, ta bayar da sanarwar cewar zasu hada gwuiwa da Obasanjo domin ceto najeriya daga halin da take ciki.

DUBA WANNAN: APC tayi babban rashi, Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalin marigayin

Yayin tattaunawar ta su, shugabannin sun amince cewar an tafka kura-kurai a baya har ma PDP ta nemi afuwar tsohon shugaban kasa Obasanjo.

Da yake karbar tuban na PDP, Obasanjo, ya bayyana cewar “hannunka baya rubewa ka yanke ka yasar” tare da bayar da tabbacin shirinsa na hada gwuiwa da duk masu kishin Najeriya domin kawo cigaba.

A jawabinsa, shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus, ya jinjinawa Obasanjo bisa jazircewarsa a kan ganin cewar Najeriya ta hau turbar da zata kai tag a tudun mun tsira.

An cimma yarjejeniyar yin aiki tare tsakanin Obasanjo da PDP

Obasanjo da shugabannin PDP

An cimma yarjejeniyar yin aiki tare tsakanin Obasanjo da PDP

An cimma yarjejeniyar yin aiki tare tsakanin Obasanjo da PDP

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel