Rashin Tsaro: An sake sabbin kashe-kashe a jihar Adamawa

Rashin Tsaro: An sake sabbin kashe-kashe a jihar Adamawa

- Kashe-kashen sun fara yawa a kasar nan, har ma sun zarta na Boko Haram

- Najeriya kasa ce da jama'arta da yawa kan bi kabilanci ko addinanci da bangaranci don rarrabe kawunansu

- Ba don akwai jami'an tsaro ba, kashe-kashe zasu qaru sosai a yankunan da kabilai kan hadu

Rashin Tsaro: An sake sabbin kashe-kashe a jihar Adamawa

Rashin Tsaro: An sake sabbin kashe-kashe a jihar Adamawa

An kashe mutane da yawa sakamakon harin dare da aka kai wa kauyuka biyar na Fulani a kudancin jihar Adamawa, mazauna da jami'an tsaro suka tabbatar da hakan.

Kamar yanda majiyar mu tace, kauyukan da aka kaiwa harin sun had a da Bidda, Wubaka, Kaurami Ngengle, Wuro Jauro ta Mayo Belwa da karamar hukumar Demsa.

Tabbatar da harin, shugaban karamar hukumar Mayo Belwa, Mohammed Bako, yace ba zai iya fadin adadin mutanenta abin ya shafa ba. Amma yace sama da gidaje 100 harin ya shafa.

"Tabbas, an kai hari kauyukan Fulani dake karamar hukuma ta, amma harin na kabilanci ne, da kabilun suka samu hatsaniya.

"Duk da jami'an tsaro kadai zasu iya fadin adadin mutanen da abun ya shafa, amma gidaje sun kone da kuma dabbobi," Mista Bako yace.

Yace yan sanda sun tafi gurin, amma sakamakon rashin kyan bangaren yasa suka kasa karasawa kauyukan da abun ya shafa.

DUBA WANNAN: Yan daba sunyi awon gaba da akwatin zabe a Ekiti

Da aka tuntubi mai magana da yawun yan sandan jihar, Othman Abubakar, yace an tura yan sanda da sojoji bangaren.

"Muna kan matsalar ne" yace.

"An kara yan sandan hana zanga zanga da sojoji don su tabbatar da komai ya koma lafiya kuma kwanciyar hankali ya tabbatar."

"Ban riga na tabbatar da yawan mutanen da abun ya shafa ba amma zan iya tabbatar muku da cewa zaman lafiya ya dawo bangaren," yace.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel