Rundunar Soji ta damke manyan dilolin kwaya a jihar Bauchi

Rundunar Soji ta damke manyan dilolin kwaya a jihar Bauchi

Dakarun Sojin Najeriya na 33 Brigade sunyi nasarar gano wasu masu sayar wa mutane da muggan kwayoyi a Yuga dake karamar hukumar Toro a Bauchi a wata simame da suka kai a Filin Kokuwa.

Wannan sanarwan da fito ne daga bakin Kakakin Hukumar Sojin, Brig Janar, Texas Chukwu, a yau Asabar 14 ga watan Yuli shekarar 2018.

Kayayakin da aka samu a hannun dilalan kwayoyin sun hada da bakar leda makil da ganyen wiwi, kuli 85 na wata ganye da ake zargin wiwi ne, wasu adadin kwayoyin Tramadol, Sholisho 'Rubber Solution' guda shida da kuma wayoyin salula guda biyar.

An kama masu sayar wa da mutane kwaya a yankin Bauchi

An kama masu sayar wa da mutane kwaya a yankin Bauchi

DUBA WANNAN: Soji sun kamo masu sayar wa da Boko Haram 'kayan aiki'

Tuni jami'an sojin sun mika su zuwa ga jami'an hukumar yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi na kasa NDLEA domin cigaba da gudanar da bincike kana daga baya sun fuskanci shari'a.

An kama masu sayar wa da mutane kwaya a yankin Bauchi

An kama masu sayar wa da mutane kwaya a yankin Bauchi

Hukumar Sojin ta kuma yi kira ga al'umma su rika sanya idanu a kan abubuwan dake faruwa a unguwaninsu kuma kada suyi kasa a gwiwa wajen sanar da hukumomin tsaro duk wani abinda basu amince dashi ba saboda a dauki mataki cikin gaggawa.

Daga karshe hukumar sojin tana kara yiwa al'umma godiya bisa irin hadin kai da ake bata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel