APC tayi babban rashi, Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalin marigayin

APC tayi babban rashi, Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalin marigayin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakonsa na ta'aziyya ga iyalin jigo a Jam'iyyar APC, Alhaji Sale Hassan, a jihar Filato da Allah ya yiwa rasuwa.

A wani jawabi da kakakin shugaba Buhari, Garba Shehu, ya raba ga manema labarai, ya bayyana tsohon dan siyasar, Marigayi Sale a matsayin mutum mai son zaman lafiya da ya dade yana kira ga jama'ar jihar Filato su zauna lafiya da juna.

APC tayi babban rashi, Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalin marigayin

APC tayi babban rashi, Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalin marigayin

DUBA WANNAN: Har ila yau: Wata gobarar dare ta kone shaguna kurmus a kasuwar garin Kano

A cewar shugaba Buhari, sakayyar da 'yan Najeriya zasu yiwa marigayin bayan mutuwar sa shine su zauna lafiya da juna.

A karshe ya yi addu'ar Allah ya ji kansa ya kuma bawa iyalinsa hakurin jure rashinsa.

A wata labarin Legit.ng ta kawo muku cewa mutame a kalla 131 ne suka rubuta takardun korafi zuwa ga kotun kasa-da-kasa ta birnin Hague a kasar Netherlands inda suka karar shugaban kasar kan gazawarsa wajen magance kashe-kashen da ake yi a wasu sassan kasar.

Wannan alkaluman dai sun fito ne daga kotun ta duniya inda ta bayyana cewa hakan na kunshe ne a cikin rahoton su na kwana-kwanan nan na binciken da suka yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel