Muhimman abubuwa 5 da suka faru a yau yayin zaben Ekiti

Muhimman abubuwa 5 da suka faru a yau yayin zaben Ekiti

A yau Asabar 14 ga watan Yuli ne 'yan takara 34 daga jam'iyyu daban-daban ke fafata a zaben gwamna a jihar Ekiti.

Tun a jiya dai an samu hargisti a jihar inda gwamnan jam'iyyar PDP mai barin gado, Ayodele Fayose, ya yi ikirarin cewa 'Yan sanda sun ci zarafinsa sai duk hukumar Yan sanda ta musanta hakan.

An fara gudanar da zaben a yankuna daban-daban a jihar kuma rahottani dake bayyana yadda zaben ke tafiya na ta bazuwa a kafafen yadda labarai. Cikin abubuwan da suka faru a yau Legit.ng ta kawo muku wasu muhimman abubuwa biyar da suka faru kamar yadda muka samu daga Vanguard.

Muhimman abubuwa 5 da suka faru a yau yayin zaben Ekiti

Muhimman abubuwa 5 da suka faru a yau yayin zaben Ekiti

1. Na'urar tattance masu kada kuri'a ta ki tattance katin zaben dan takarar jam'iyyar PDP, Farfesa Olusola Eleka.

2. An kuma samu rahotannin cewa an raba wa masu kada kuri'a N4000 domin su zabi wasu jam'iyyu

DUBA WANNAN: 2019: Secondus da wasu jiga-jigan PDP zasu gana da Obasanjo a yau

3. Har ila yau, na'urar tattance masu kada kuri'ar ta ki tattance katin uwargidan dan takarar jam'iyyar APC, Fayemi Kayode.

4. Wani mutum mai suna Kazeem da ya gabatar da kansa a matsayin agent din APC ya tafi rumfar kada kuri'a dake yankin Igbemo a karamar hukumar Irepodun-Ifelodin ta jihar inda ya yi barazanar datse yatsun duk wanda ya zabi PDP. Hakan ya janyo tarzoma amma daga baya jami'an tsaro sun shawo kan matsalar.

5. A gunduma ta 10, rumfar zabe mai lamba 003, a Fajuyi Ado-Ekiti, wani shugaban 'yan sanda ya dauke 'yan sanda biyu dake kula da zaben ya tafi dasu a cikin wata mota.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku cigaba ba biyo mu domin samun karin bayani ...

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel