Zaben Ekiti: An samu hargitsi yayin da aka yi barazanar datse hannun duk wanda ya zabi jam'iyyar adawa

Zaben Ekiti: An samu hargitsi yayin da aka yi barazanar datse hannun duk wanda ya zabi jam'iyyar adawa

An samu tangarda a rumfar kada kuri'a mai lamba 012 dake yankin Igbemo a karamar hukumar Irepodun-Ifelodin ta jihar Ekiti yayin da wani mutum da ya gabatar da kansa a matsayin agent duk da cewa bai saka kayan agent ba ya fara yiwa jam'iyyarsa kamfe.

Mutumin da yace sunanan Kazeem ya iso rumfar zaben misalin karfe 9 na safe lokacin an fara kada kuri'a.

Kazeem ya yi magana da yaren mutanen kauyen, ya shawarci mutanen su zabi dan takarar jam'iyyar APC, Kayode Fayemi, ya kuma yi gargadin cewa zai guntule yatsun duk wanda ya sake ya jefa wa jam'iyyar adawa.

Ekiti: 'Za'a guntule yatsun hannun duk wanda ya dangwalawa PDP"

Ekiti: 'Za'a guntule yatsun hannun duk wanda ya dangwalawa PDP"

DUBA WANNAN: Yadda wani dan shekaru 17 ya tsira daga gidan matsafa a Kano

"Ku zabi APC. Zan guntule yatsun hannun duk wanda ya zabi PDP," Abinda ya rika maimaitawa kenan.

Wannan kalaman ya fusata wani mai jefa kuri'a, Mr Ojo, har ya tasan ma Kazeem ta fada.

Bisa ga dukkan alamu Mr. Ojo masoyin jam'iyyar PDP ne hakan yasa ya kallubalanci Kazeem.

Saboda ya nuna masa ba wasa ya keyi ba, Mr. Ojo ya dako wata katako ya nufi Kazeem da ita yana son ya buge shi da ita.

Wannan hayaniyar tasu ya sanya an dakata jefa kuri'an na tsawon wani lokaci. Sai dai daga baya, jami'an tsaro sun hallarto wajen jefa kuri'an kuma suka kwantar da tarzomar.

Wasu mutane a wajen su shaida wa Premium Times cewa Kazeem ya hallarci rumfunan jefa kuri'a biyu yana yin irin wannan barazanar sai dai Premium Times ba ta da tabbacin hakan ya faru a wasu wuraren jefa kuri'ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel