Jerin mutanen da PDP ta fitar da zasu gana da Obasanjo da kuma dalilin ganawar su

Jerin mutanen da PDP ta fitar da zasu gana da Obasanjo da kuma dalilin ganawar su

Mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP karkashin shugabanta na kasa, Uche Secondus, zasu gana da Obasanjo a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, a yau, Asabar.

Dakarun 'ya'yanta da PDP ta ware domin ganawa da Obasanjo sun hada da, shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar, The Walid Jubrin, Cif Bode George, da tsohon shugaban majalisar dattijai, Sanata Adolphus Wabara. Tuni dukkansu suka isa jihar Ogun tun jiya.

Jerin mutanen da PDP ta fitar da zasu gana da Obasanjo da kuma dalilin ganawar su

Jerin mutanen da PDP ta fitar da zasu gana da Obasanjo da kuma dalilin ganawar su

DUBA WANNAN: 2019: Secondus da wasu jiga-jigan PDP zasu gana da Obasanjo a yau

Da yake ganawa da manema labarai, shugaban jam'iyyar PDP, Secondus, ya bayyana cewar zasu gana da "jarumi" kuma "gwarzo" Obasanjo domin bashi karfin gwuiwa da goyon bayan cigaba da gwagwarmayar kwace mulki daga hannun jam'iyyar APC mai mulki.

"Ganawar ba ta da wata manufa ta kashin kanmu. Mun zabi ganawa da Obasanjo ne saboda mutum ne gwarzo, jarumi kuma mai nasara. A saboda haka muka ga ya dace mu nuna masa goyon bayanmu tare da bashi karfin gwuiwa a gwagwarmayar sa ta ganin an canja gwamnatin APC," in ji Secondus.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel