Zaben Ekiti: An baza 'yan sanda 30,000, helikwatoci 2 da motocin sulke 5 don tabbatar da tsaro

Zaben Ekiti: An baza 'yan sanda 30,000, helikwatoci 2 da motocin sulke 5 don tabbatar da tsaro

Kamar yadda muka samu, akalla jami'an tsaro dubu 30 ne da jirage masu saukar angulu biyu hadi da motocin sulke biyar ne aka baza domin tabbatar da tsaro a zaben da ke gudana a jihar Ekiti a yau dinnan.

Wannan dai na zama kari ga motocin sintiri akalla 250 da kuma aka baza a dukkan wuraren zaben a kananan hukumomi 16 dake a fadin jihar duk domin tabbatar da doka-da-oda.

Zaben Ekiti: An baza 'yan sanda 30,000, helikwatoci 2 da motocin sulke 5 don tabbatar da tsaro

Zaben Ekiti: An baza 'yan sanda 30,000, helikwatoci 2 da motocin sulke 5 don tabbatar da tsaro

KU KARANTA: Mun hakura da samun shugabanci mai kyau daga Buhari - Babbab malamin addini

Legit.ng ta samu cewa sai dai wannan matakin na baza jami'an tsaro bai yi wa wasu dayawa musamman ma dai 'yan PDP a jihar dadi ba inda suka yi zargin cewa hakan zai razana masu zabe ne kawai.

A wani labarin kuma, Kotun duniya ta kasa-da-kasa dake a birnin Hague, a kasar Netherlands ta bayyana cewa kawo yanzu ta samu takardun korafi akalla 131 daga jama'a daban daban a Najeriya game da gazawar gwamnatin shugaba Buhari a fannin tsaro.

Wannan alkaluman dai sun fito ne daga kotun ta duniya inda ta bayyana cewa hakan na kunshe ne a cikin rahoton su na kwana-kwanan nan na binciken da suka yi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel