Mun yanke kuna da samun kyakkyawan shugabanci daga Buhari - Wani babban malamin addini

Mun yanke kuna da samun kyakkyawan shugabanci daga Buhari - Wani babban malamin addini

Shugaban majami'un darikar Roman Katolika na garin Abuja, babban binin tarayya mai suna Olaiyekan ya bayyana cewa bishop-bishop din Najeriya tuni suka yanke kauna da samun shugabanci na gari daga shugaba Buhari.

John Cardinal ya bayyana hakan ne a garin Ilorin na jihar Kwara lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala nadin shugaban majami'un Roman Katolikan jihar Bishop Paul Olawoore.

Mun yanke kuna da samun kyakkyawan shugabanci daga Buhari - Wani babban malamin addini

Mun yanke kuna da samun kyakkyawan shugabanci daga Buhari - Wani babban malamin addini

KU KARANTA: "PDP tamkar aljanna ce a Najeriya"

Legit.ng ta samu cewa ya kara da cewa kafin zuwan wannan gwamnatin sun yi tsammanin za su samu shugabanci na gari amma sai lamarin ya zo masu ba haka ba.

Haka zalika ya koka kan yadda rayukan 'yan Najeriya suka zama kamar na kiyashi inda yace ana ta kashe-kashe sannan kuma gwamnatin tarayya ta nuna halin-ko-in-kula da lamarin.

A wani labarin kuma, Kotun duniya ta kasa-da-kasa dake a birnin Hague, a kasar Netherlands ta bayyana cewa kawo yanzu ta samu takardun korafi akalla 131 daga jama'a daban daban a Najeriya game da gazawar gwamnatin shugaba Buhari a fannin tsaro.

Wannan alkaluman dai sun fito ne daga kotun ta duniya inda ta bayyana cewa hakan na kunshe ne a cikin rahoton su na kwana-kwanan nan na binciken da suka yi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel