Rana bata karya: Ga dukkan abunda ya kamata ku sani game da zaben gwamna a jihar Ekiti da ke gudana yau

Rana bata karya: Ga dukkan abunda ya kamata ku sani game da zaben gwamna a jihar Ekiti da ke gudana yau

Gari fa ya dauki harami a can kudu maso gabashin Najeriya inda yanzu haka ake ta shirye-shiryen kada kuri'a a zaben da aka sa ranar zai gudana a yau din nan domin samun wanda zai maye gurbin Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu shine cewa ana zaman dar-dar ne a garin biyo bayan jami'an tsaro 30,000 da aka baza a dukkan fadin jihar.

Rana bata karya: Ga dukkan abunda ya kamata ku sani game da zaben gwamna a jihar Ekiti da ke gudana yau

Rana bata karya: Ga dukkan abunda ya kamata ku sani game da zaben gwamna a jihar Ekiti da ke gudana yau

KU KARANTA: Wani matashin dan arewa ya samu mukami a babban bankin duniya

Legit.ng ta samu cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ma dai watau INEC ta bayyana cewa jihar mai kananan hukumomi 16 tana da rumfunan zabe 2,195 sannan kuma mutane akalla 913,333 ne suka yi rijistar zaben.

Sai dai kuma daga cikin su, mutane 667,270 ne yanzu haka aka tantance cewa za su iya kada kuri'un su a zaben na yau da za'a gudanar a tsakanin 'yan takara 34.

Wasu daga cikin wadanda ke takarar zama gwamnan dai sune na jam'iyyar Accord Party, Jacob Aluko, sai kuma na jam'iyyar All Progressives Congress candidate, Kayode Fayemi, da kuma na jam'iyyar Peoples Democratic Party candidate, Kolapo Olusola.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel