Kashe-kashe: Mutane 131 ne suka kai karar gwamnatin Buhari a kotun kasa-da-kasa

Kashe-kashe: Mutane 131 ne suka kai karar gwamnatin Buhari a kotun kasa-da-kasa

Kotun duniya ta kasa-da-kasa dake a birnin Hague, a kasar Netherlands ta bayyana cewa kawo yanzu ta samu takardun korafi akalla 131 daga jama'a daban daban a Najeriya game da gazawar gwamnatin shugaba Buhari a fannin tsaro.

Wannan alkaluman dai sun fito ne daga kotun ta duniya inda ta bayyana cewa hakan na kunshe ne a cikin rahoton su na kwana-kwanan nan na binciken da suka yi.

Kashe-kashe: Mutane 131 ne suka kai karar gwamnatin Buhari a kotun kasa-da-kasa

Kashe-kashe: Mutane 131 ne suka kai karar gwamnatin Buhari a kotun kasa-da-kasa

KU KARANTA: "PDP tamkar aljanna ce a siyasar Najeriya"

Legit.ng ta samu cewa manya daga cikin koke-koken sune wadanda suka fito game da kisan farar hulan dake yi a arewa maso gaban da sunan yaki da 'yan Boko Haram da kuma kashe 'yan shi'a.

Sauran sun hada da kashe-kashen da ake ta yi sakamakon fadan makiyaya da manoma a yankunan tsakiyar Najeriya da kuma 'yan tada kayar baya na Biyafara a shekarar da ta gabata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel