2019: Secondus da wasu jiga-jigan PDP zasu gana da Obasanjo a yau

2019: Secondus da wasu jiga-jigan PDP zasu gana da Obasanjo a yau

Mambobin kwamitin gudananarwa na kasa na jam'iyyar PDP zasu gana da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a gidansa dake Abeokuta a yau Asabar gabanin zaben gwamna da za'ayi a jihar Ekiti.

Shugaban PDP na kasa, Uche Secondus ne bayar da sanarwan yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan wata taron da 'yan kwamitin zartarwa reshen jihar Ogun na jam'iyyar suka gudanar tare da 'yan kwamitin gudanarwar.

2019: Secondus da wasu jiga-jigan PDP zasu gana da Obasanjo

2019: Secondus da wasu jiga-jigan PDP zasu gana da Obasanjo

Secondus yace ya zama dole su gana da Obasanjo saboda shi gwarzo ne wanda ya sha gumurzu a baya sakamakon irin kwaraniyar da ya sha a tarihinsa na siyasa da shugabanci don ya basu shawarwari.

DUBA WANNAN: An kama wani dattijo a Katsina dake yiwa barayin shanu safarar bindigogi

Duk da irin bayannan da gwamnatin tarayya tayi game da yadda zata kasafta kudaden Abacha da aka karbo a kasashen waje, Secondus ya soki gwamnatin inda yace kawai za'a yi rabon kudin ne ba tare da tsari ba.

Za'a fara rabawa talakawan Najeriya kudaden ne a cikin wannan watar ta Yuli kamar yadda gwamnatin tarayyar ta bayyana a baya.

Shugaban shirin jin dadi da walwalar ta gwamnatin tarayya (SIP), Maryam Uwais, tace gwamnatin tarayyar tayi wata yarjejeniya da Bankin Duniya kan yadda za tayi rabon kudin.

A cewar Uwais, jihohi 18 ne zasu amfana da kudaden, jihohin sune Neja, Kogi, Ekiti, Oyo, Osun, Kwara, Cross Rivers da Bauchi. Sauran sun hada da Jigawa, Gombe, Benue, Taraba, Adamawa, Kano, Katsina, Kaduna, Nasarawa da Anambra.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel